Babu wani toshiyar baki da na samu daga Buhari – Saraki

Babu wani toshiyar baki da na samu daga Buhari – Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki, yayi watsi da rade-radin cewa fadar shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun bashi toshiyar baki don ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar.

Ya bayyana cewa duk da cewar suna ta tattaunawa kan wasu lamuran kasa, batun cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da APC sun gabatar masa da toshiyar baki ba gaskiya bane.

Kafafen yada labarai sun rahoto cewa fadar shugaban kasa, da shugaban APC, Adams Oshiomhole sun gabatar da toshiyar baki don hana yan sabuwar APC sauya sheka.

Babu wani toshiyar baki da na samu daga Buhari – Saraki

Babu wani toshiyar baki da na samu daga Buhari – Saraki

Sai dai a wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin ta hannun Mista Yusuph Olaniyonu, hadiminsa na musamman a kafafen yada labarai, Saraki yace babu abu makamancin haka da faru.

KU KARANTA KUMA: R-APC: Ina baccina harda munshari – Oshiomhole

Ya bayyana cewa makomar kasar da damokradiyarta na cikin hatsari, ba wai lamarin bayarwa ko karba bane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel