Girman kan Fayose da gudunmawar Makarfi suka jawo mana asarar kujerar gwamna a zaben Ekiti – Sanata Buruji

Girman kan Fayose da gudunmawar Makarfi suka jawo mana asarar kujerar gwamna a zaben Ekiti – Sanata Buruji

Sanatan jihar Ogun ta gabas, Buruji Kasahamu,ya dora alhakin faduwar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ekiti a kan girman kan gwamna Fayose.

Kashamu, dan PDP, ya bayyana cewar tun kafin zaben na ranar 14 ga watan Yuli, ya hango wa jam’iyyar faduwa saboda mutanen jihar Ekiti sun kosa da halin Fayose.

Ya kara da cewa, “babu abinda zai hana PDP faduwa zaben musamman idan aka yi la’akari da yadda tsohon shugaban jam’iyya Ahmed Makarfi ya bawa Fayose dammar cin mutuncin ‘yan PDP daga yankin kudu maso yamma, dalilan day a saka da yawan ‘yay’an jam’iyyar ficewa.”

Girman kan Fayose da gudunmawar Makarfi suka jawo mana asarar kujerar gwamna a zaben Ekiti – Sanata Buruji

Fayose da Makarfi

Sannan ya cigaba da cewa, “ba don jama’ar jihar Ekiti sun gaji da halin Fayose ba, babu yadda za a yi ya fadi har a karamar hukumarsa.

Fayose tamkar kansa ne a jam’iyyar PDP kuma tunda jam’iyya ba zata iya daukan wani mataki a kansa ba, jama’ar jihar sa sun taimake mu sun kawar da shi, a cewar Kashamu.

DUBA WANNAN: Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa

Kashamu na wadannan kalamai ne a karshen mako yayin ganawa da manema labarai.

Sanatan ya bukaci shugabancin PDP day a gaggauta daukan matakan hana jam’iyyar durkushewa a yankin kudu maso yamma kafin zaben shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel