Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Watanni bayan tattaunawa da neman matsaya, shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara da sauran mambobin jam’iyyar APC mai mulki da ke korafe-korafe na iya sauya sheka daga jam’iyyar a ranar Alhamis.

A makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran shugabannin jam’iyyar sun gaza shawo kan shugaban majalisar dattawa da ya sake duba batun barin jam’iyya mai mulki.

Saraki ya hadu da Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a fadar shugaban kasa a Abuja.

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Wata majiya a taron ta bayyana cewa an ba Saraki damar zabar duk wani matsayi da yake so a gwamnatin APC na gaba, amma ya basar.

KU KARANTA KUMA: R-APC: Ina baccina harda munshari – Oshiomhole

“Ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta tozarta shi a shekaru uku da suka gabata, sannan kuma cewa sanya bakinsu ya zo a kurarren lokaci,” cewar majiyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel