Hukumar NSITF: Oshiomhole yayi barazanar dakatar da Ngige daga APC

Hukumar NSITF: Oshiomhole yayi barazanar dakatar da Ngige daga APC

Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole a ranar Litinin, yayi barazanar dakatar da ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, daga jam’iyyar idan ya ki kaddamar da mambobin hukumomin tarayya.

Oshiomhole yayi wannan barazana ne a wani hira da manema labarai a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya ce APC karkashin jagorancinsa bazata ci gaba da zuba ido tana kallon ministoci masu amfani da matsayinsu wajen tozarta shugaban kasa Muhammadu Buhari bat a hanyar kin aiwatar da umurninsa.

Ngige ya karya dokar kundin tsarin mulki da nada mambobin hukumomin tarayya karkashin ma’aikatar sa.

Oshiomhole a wata wasika ya ba ministan kwadagon mako guda domin ya kaddamar da hukumomin dake ma’aikatarsa.

The parastatals and agencies are the Nigeria Social Insurance Trust Fund, National Directorate of Employment, National Productivity Centre, and Michael Imoudu Institute for Labour Studies.

Hukumomin sune, Nigeria Social Insurance Trust Fund, National Directorate of Employment, National Productivity Centre, da kuma Michael Imoudu Institute for Labour Studies.

KU KARANTA KUMA: A 2019, yan Najeriya za su yi jana’izar PDP – Hadimar Buhari

Sai dai Ngige ya bayyana dalilin da yasa ba zai kaddamar da su cikin mako guda da aka basa ba.

Ya nuna rashin amincewarsa ga cewa irin wannan wasika zai fito daga shugaban APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel