Wasu dalilai ne suka kai ni ga lalata karamar yarinya – Inji dan shekara 52

Wasu dalilai ne suka kai ni ga lalata karamar yarinya – Inji dan shekara 52

Jami’an yan sandan jihar Cross River sun kama wani mutumi mai shekaru 52, Henry Oboh bisa zargin lalata yarinya yar shekara 12 a wani kari mai suna ‘One Man’ a karamar hukumar Atamkpa dake jihar.

Oboh ya ja yarinyar zuwa dakinsa sannan yayi barazanar soka mata wuka kafin yayi lalata da ita.

Mai laifin wanda aka gurfanar tare da sauran masu laifi, kan laifuka daban-daban a hedkwatar yan sanda dake Calabar, yace wasu dalilai ne suka tunzura shi har ya aikata laifin.

Oboh, wanda ya kasa bayyana dalilan, yace bai taba shirin lalata mai laifin ba, inda ya kara da cewa ya shirya fuskantar shari’ kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

Mutumin mai yara hudu yace ya yi danasanin aikata abun day a aikata, cewa ya bayar da kansa a kama sannan a yi bincike saboda bayan ya aikata laifin ne ya gane cewa bai kyauta ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel