Yanzu Yanzu: Yan takarar kujerar gwamna 13 karkashin lemar PDP sun ki amincewa da Ortom

Yanzu Yanzu: Yan takarar kujerar gwamna 13 karkashin lemar PDP sun ki amincewa da Ortom

Yan takarar kujerar gwamna guda goma sha uku karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 a jihar Benue sun ki amincewa da dawwar Gwamna Samuel Ortom jam’iyyar.

Da suke jawabi a taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, yan takaran sun bayyana cewa ba wai ba sa maraba da masu sauya sheka bane; sai dai basa maraba da mutane masu mugun nufi duk da sun bayyana Ortom a matsayin wani nauyi.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

“Gwamnan jihar Benue a yau ya kasance wani nauyi, ba wai kadara ba. Bama maraba da shi,” cewar John Tondu, daya daga cikin yan takaran.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel