APC ta tafka mummunan rashi a jihar Osun

APC ta tafka mummunan rashi a jihar Osun

- Wani jigo a jam'iyyar APC ya dangwarar da tsitsiyarsa

- Sai ana zargin ya sauya shekar ne don yin takarar gwamna a jiharsa

Sakataren gwamnatin jihar Osun Alhaji Moshood Adeoti, ya sauya sheka daga jamiyyar APC zuwa jamiyyar ADP domin yin takarar gwamna.

APC ta tafka mummunan rashi a jihar Osun

APC ta tafka mummunan rashi a jihar Osun

A ranar Juma'a ne Adeoti ya dangwarar da shahadar tasa yayinda ake gaf da shiga zaben fidda gwani da jamiyyar APC ta gudanar, inda yayi zargin an shirya wata makarkashiyar da zata baiwa shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Osun Alhaji Gboyega Oyetola nasarar zama dan takara.

KU KARANTA: Yau shekaru 4 dai-dai da aka kaiwa Buhari harin Bam a Kaduna, karanta abinda ya faru (Bidiyo)

Tsohon dan jamiyyar APC din ya isa shelkwatar sabuwar jamiyyar da ya koma wato ADP inda dubban magoya bayansa suka kama ihu da murnar zuwansa.

Ana kallon komawarsa cikin jam’iyyar ADP nada alaka da kudurinsa na neman takarar gwamna da ya himmatu da yi.

Jam’iyyar APC dai na fama da rikice-rikicen cikin gida wanda ya sanya da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel