PDP na rokon Akpabio da kada ya koma APC

PDP na rokon Akpabio da kada ya koma APC

Alamu sun nuna cewa Sanata Godswill Akpabio na iya komawa jam’iyyar ruling All Progressives Congress (APC) kwannan nan.

An tattaro cewa jam’iyyar PDP na duk kokarin da zatayi domin hada sanatan komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Wata majiya daga PDP ta fadama jaridar Nation cewa shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, ya sanya Akpabio a kwana a gidansa dake Asokoro Abuja a karshen mako kan lamarin.

PDP na rokon Akpabio da kada ta koma APC

PDP na rokon Akpabio da kada ta koma APC

Akwai rahotannin cewa an samu sabani tsakanin Akpabio da gwamnan sa bayan zargin cewa Emmanuel baya son bude wani gini na Sharaton otel, Ikot Ekpene wanda Akpabio ya gina ya kuma cike kayan alatu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Yan takarar kujerar gwamna guda goma sha uku karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 a jihar Benue sun ki amincewa da dawwar Gwamna Samuel Ortom jam’iyyar.

Da suke jawabi a taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, yan takaran sun bayyana cewa ba wai ba sa maraba da masu sauya sheka bane; sai dai basa maraba da mutane masu mugun nufi duk da sun bayyana Ortom a matsayin wani nauyi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel