Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

Kakakin kungiyar sabuwar APC, Kassim Afegbua a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli ya yi Allah wadai da gwamnatin tarayya kan zargin yadda ake wulakanta shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki gabannin zaben 2019.

Channels TV ta ruwaito cewa Afegbua ya nuna bacin rai kan yadda ake yiwa Saraki tunda aka fara shari’arsa a kotun CCT wadda ya kwashe tsawon shekaru uku.

A cewarsa, “Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa rikakken dan siyasa ne. Sannan yana daga cikin wadanda suka tabbatar da cewa gwamnatin nan tayi nasara a 2015.

Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

Kungiyar sabuwar APC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ake yiwa Saraki

“An yasar da shi cikin sanyi, an daura masa laifi, an tozarta shi, an maida shi abun dariya. An kira shi da sunaye daban-daban. A lokacin da kotun koli ta wanke shi akan zargi da ake yi masa, sai ya zamo tamkar amarya.”

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

Wannan kalamai na Afegbua na zuwa ne makonni biyu bayan kotun koli ta wanke Saraki daga zarge-zarge da ake yi masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel