Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - Kawu Baraje

Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - Kawu Baraje

- Jam'iyyar APC na gab da fuskantar ficewar 'yan tsagin R-APC daga cikinta

- Bayan samun sauyin shugabanci a APC karkashin Adams Oshiomhole, ana sanya rai zai shawo kan rikicin cikin gidan, amma sai dai hakan na kokarin gagara

Jagoran mambobin jamiyyar R-APC Alhaji Kawu Baraje ya bayyana cewa sun yanke hukuncin fita daga jamiyyar APC gaba daya.

Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - In Kawu Baraje

Mun yanke shawarar barin jamiyyar APC - In Kawu Baraje

Barajen dai ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin tsagin jamiyyar R-APC Kassim Afegbua, inda ya ce kokarin da shugaba Muhammad Buhari yake yi tare da shugaban jamiyyar na kasa Adams Oshiomhole na ganin ba su fita daga jamiyyar ba, hakika sun makara domin bakin alkalami ya bushe.

KU KARANTA: Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

Afegbua ya ce ba za su taba gasgata abinda shugabancin jamiyyar ta APC ya ke alkawarta musu ba, domin kuwa ba su da alkawari.

A daya bangaren kuma Alhaji Kawu Baraje ya bayyana cewa babu wani matsayi ko mukami da za'a baiwa mambobin tsagin jamiyyar ta R-APC da zai wanke su daga batancin da jam’iyyar APC ta yi musu.

"Mun yanke hukuncin barin jamiyyar APC ko da kuwa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki zai cigaba da zama a cikinta, to hakan zabinsa ne amma babu wani mai goyon bayansa da zai zauna tare da shi" A cewar Barajen a garin Ilorin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel