Barazanar yaki: Donald Trump ya mayarwa Hassan Rouhani martini mai zafi

Barazanar yaki: Donald Trump ya mayarwa Hassan Rouhani martini mai zafi

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya mayarwa shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, martini mai zafi a shafin Tuwita kan gargadin da Rouhani ya masa.

Game da cewar CNN, shugaban kasar Amurka ya mayar da martanin ne cikin dare kan jawabin shugaban kasar Iran da yace: “ Zaman lafiya da Iran babban zaman lafiya ne da kowa, hakazalika yaki da Iran uwar yakoki ne,…. Kada kayi wasa da bindin Zaki, inda ba haka a za kayi nadama”.

Trump yace: “ Ga shugaban kasar Iran Hassan Rouhani: Kada ka sake barazana ga kasar Amurka, idan ba haka ba za ka ga sakamakon haka kamar yadda ka gani a tarihi. Mun fita daga kasar da za ta yarda da maganganun yaki da mutuwa. Kayi hattara”

KU KARANTA: Ku gayawa Buhari ya fara shirin tattara komatsan sa ya nufi Daura inji PDP

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa Iran, Hassan Rouhani, ya gargadi takwararsa na Amurka, Donald Trump, kan take-taken da yake masa.

Rouhani ya ja kunnen Trump kan kokarin tada hankalin kasarsa inda ya ce fito-na-fito da kasar Iran uwar dukkan yakoki ne kuma ba za tayi kyau ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel