2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

Kungiyar amintattu da na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP za su yi taron gaggawa a ranar Litinin, 23 ga watan Yuli, domin tattauna bukatun wasu mambobin sabuwar jam’iyyar hadin gwiwa wato Coalition of United Political Parties (CUPP).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron za su tattauna akan zabar dan takarar shugaban kasa mai karfi guda daya domin yiwa jam’iyyar takara a 2019, da kuma bukatar da wasu yan kungiyar sabuwar APC suka gabatar.

Jam’iyyar ta amince da fitar da dantakara guda daya da zai tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.

Jam’iyyar PDP kadai na da yan takara sama da guda 15 yayinda jam’iyyun siyasa da dama da suka shiga yarjejeniyar ma suke da nasu yan takaran.

2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

2019: PDP ta kira taron masu ruwa da tsaki na gaggawa kan bukatar R-APC

Bukatun da kungiyar sabuwar APC ta gabatar sun hada da bukatar PDP ta canja sunanta domin inganta martabarta sannan kuma aa ba mambobinsu dake rike da mukamai a yanzu haka a majalisun jihohi da na kasa baki daya tikiti.

KU KARANTA KUMA:

Wani mamba a kungiyar amintattu na PDP, da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa taron za su tattauana akan yadda za su tarbi masu sauya sheka zuwa jam’iyyar a cikin makon nan.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel