Yanzu-yanzu: Dan kunar bakin wake ya kai mumunan hari Masallaci da asuban nan

Yanzu-yanzu: Dan kunar bakin wake ya kai mumunan hari Masallaci da asuban nan

Wani dan kunar bakin waken yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram ya kai mumunan harin kunar bakin wani masallaci da ke Konduga a jihar Borno lokacin Sallar Asuba misalin karfe 5:15 na safe.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar The Cable cewa an hallaka masallata da dama kuma wasu sun jikkata.

Yayinda jami’an tsaro suka hallaro wajen a yanzu, an garzaya da wadanda suka jikkata asibiti.

A yanzu dai mutane takwas ne suka rasa rayukansu game da cewar wani dan CTJF a garin, Ibrahim Liman, wanda yayi bayani ga manema labarai.

Ya bayyana cewa dan kunar bakin wake ne ya shigo masallacin misalin karfe 5:15 yayinda mutane ke Sallah ya tayar da Bam.

KU KARANTA: Wani ‘Dalibi ya zagi Annabi Muhammad a makarantar koyon shari’a da ke Legas

Yace: “Wani dan kunar bakin wake ne ya shiga masallacin misalin karfe 5:15 yayinda ake Sallah ya tayar da Bam. Ya kashe mutane takwas tare jikkata wasu biyar.”

Mutane bakwai suka mutu a take cikin masallacin yayinda daya ya cika a hanyar asibitin Maiduguri.”

Wani mazaunin garin Umar Goni ya bayyana cewa yana hanyar zuwa masallacin ne Bam din ya tashi kuma ya taimaka wajen ceton mutane tare da jami'an CJTF.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel