Mi'ara koma-baya: Matatun man Kaduna da Fatakawal sun tsaya cak, sun dena aiki

Mi'ara koma-baya: Matatun man Kaduna da Fatakawal sun tsaya cak, sun dena aiki

A cikin wani daftarin rahoto game da yanayin da matatun man kasar nan suke ciki da kamfanin albarkatun man fetur na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC ya fitar, ya bayyana cewa matatun man fetur din garin Kaduna da na Fatakwal sun tsaya cak.

Sai dai kuma daftarin rahoton ya bayyana cewa kawo yanzu matatar man garin Wari na jihar Delta tana aikin gadan-gadan yadda yakamata fiye da da ma.

Mi'ara koma-baya: Matatun man Kaduna da Fatakawal sun tsaya cak, sun dena aiki

Mi'ara koma-baya: Matatun man Kaduna da Fatakawal sun tsaya cak, sun dena aiki

KU KARANTA: Ko kun san babban mai tsaron lafiyar Shugaba Buhari

Legit.ng dai ta samu cewa a kwanan baya jim kadan bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari mulkin kasar dai matatun man sun soma aiki dukkan su a matakin da ya dauka na cika alkawuran da ya daukar wa yan Najeriya a lokacin yakin neman zaben sa a 2015.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta bukaci talakawan Najeriya da su kai sakon su zuwa ga Buhari na cewa tun wuri ya ma fara shire-shiren tattara kayan sa domin tafiya mahaifar sa ta Daura a shekarar 2019.

Jam'iyyar dai ta yi wannan kiran ne a wani martani da ta maidawa fadar shugaban kasar game da kiran da yayiwa 'yan Najeriya da su je su yankin katin zabe domin samun damar jefa kuri'ar su a zaben mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel