Ku gayawa Buhari ya fara shirin tattara komatsan sa ya nufi Daura inji PDP

Ku gayawa Buhari ya fara shirin tattara komatsan sa ya nufi Daura inji PDP

Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta bukaci talakawan Najeriya da su kai sakon su zuwa ga Buhari na cewa tun wuri ya ma fara shire-shiren tattara kayan sa domin tafiya mahaifar sa ta Daura a shekarar 2019.

Jam'iyyar dai ta yi wannan kiran ne a wani martani da ta maidawa fadar shugaban kasar game da kiran da yayiwa 'yan Najeriya da su je su yankin katin zabe domin samun damar jefa kuri'ar su a zaben mai zuwa.

Ku gayawa Buhari ya fara shirin tattara komatsan sa ya nufi Daura inji PDP

Ku gayawa Buhari ya fara shirin tattara komatsan sa ya nufi Daura inji PDP

KU KARANTA: An ce wai Muammar Gaddafi na nan da ran sa

Legit.ng ta samu cewa sai dai jam'iyyar a martanin nata ta ce da ma sun dena bata yawun bakin su domin kuwa gazawar da sukayi a cikin mulkin su ma kadai ta isa ta sa talakawa yankar katin zaben su don su kore su ba sai sun yi ta shelanta hakan ba.

A wani labarin kuma, A cikin wani daftarin rahoto game da yanayin da matatun man kasar nan suke ciki da kamfanin albarkatun man fetur na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC ya fitar, ya bayyana cewa matatun man fetur din garin Kaduna da na Fatakwal sun tsaya cak.

Sai dai kuma daftarin rahoton ya bayyana cewa kawo yanzu matatar man garin Wari na jihar Delta tana aikin gadan-gadan yadda yakamata fiye da da ma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel