Matashi zai hadu da Atiku Abubakar bayan yayi wani zane mai kama da shi

Matashi zai hadu da Atiku Abubakar bayan yayi wani zane mai kama da shi

- Atiku Abubakar zai hadu da wani Saurayi mai hikima da ya zana shi

- Wani ‘Dalibin Jami’ar ABU dai ne ya zana Atiku Abubakar a takarda

Labari ya zo mana cewa wani ‘Dalibi da ke karatu a fitacciyar Jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya a Jihar Kaduna mai suna Ishaq Madaki zai hadu da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.

Matashi zai hadu da Atiku Abubakar bayan yayi wani zane mai kama da shi

Yadda wani Bawan Allah ya zana Atiku Abubakar

Wannan Matashin Dalibi ya samu shiga wajen Atiku ne bayan da ya zana tsohon Mataimakin Shugaban Kasar a takarda. Zanen wannan ‘Dalibi ya ba Jama’a sha’awa ainun don haka aka jawo hankalin Atiku domin ya gani da kan sa.

KU KARANTA: Kasurguman Attajirai 3 da ake ji da su a Najeriya a 2018

Matashi zai hadu da Atiku Abubakar bayan yayi wani zane mai kama da shi

Yada Atiku Abubakar ya nemi ya gana da wanda ya zana sa

An kuwa yi dace tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya ga wannan zane mai ban kaye bayan an nuna masa. Nan-take babban ‘Dan siyasar yace zanen ya ba shi sha’awa kuma zai so ya hadu da wannan yaro mai ‘dan karen hikima.

Wannan ‘Dalibi na Jami’ar ta Zariya mai suna Ishaq Madaki dai na daf da cika burin sa na haduwa da babban ‘Dan siyasar. Ko da ya zana Atiku sai ya nemi jama’a a shafin sadarwa na zamani Tuwita su taya su nuna masa kuma aka dace.

Hakan na zuwa ne bayan da ku ka ji cewa guguwar Atiku ta rusa Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa. Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi wa APC illa a Arewa inda wasu manyan ‘Yan siyasan Adamawa su ka dawo PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel