Hukumar JAMB ta sa Biliyan 7.8 a asusun Gwamnatin Tarayya

Hukumar JAMB ta sa Biliyan 7.8 a asusun Gwamnatin Tarayya

- An kuma tatsowa Gwamnatin Tarayya kudi a Hukumar JAMB ta kasa

- Wannan shekarar JAMB ta yi shirin maidawa Najeriya kudi Biliyan 7

- Gwamnatin Kasar ta nemi Hukumar ta kashe Biliyan 2 daga cikin kudin

Mun samu labari cewa Hukumar jarrabawar shiga Makarantun gaba da Sakandare ta kasa watau JAMB ta maida wasu makudan kudi da su ka haura Biliyoyi zuwa asusun Gwamnatin Najeriya.

Hukumar JAMB ta sa Biliyan 7.8 a asusun Gwamnatin Tarayya

Shugaban Hukumar JAMB ya samawa Gwamnatin Najeriya kudin shiga

A kwanan nan ne Hukumar JAMB ta tatsowa Gwamnatin Tarayya kudi Naira Biliyan 7.8 kamar yadda babban Jami’in yada labarai na Hukumar watau Fabian Benjamin ya bayyanawa ‘Yan jarida jiya Lahadi a Garin Legas.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya ci amanar mu a tafiyar siyasa - Buba Galadima

Fabian Benjamin ya bayyana cewa Hukumar ta JAMB ta yi irin abin da tayi ne a shekarar bara watau 2017 inda ta maidawa Gwamnatin Tarayya rarar duk kudin da aka samu daga wajen rajistar jarrabawar UTME da aka yi bana.

JAMB ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta karbi Naira Biliyan 5.6 ne kurum daga cikin kudin inda aka amince su yi amfani da ragowar kudin wajen gyara Hukumar domin ganin ta shiga sahun Hukumomin da ake ji da su.

Daga hawan sabon Shugaban JAMB zuwa yanzu, Hukumar ta maidawa Najeriya kudi fiye da Biliyan 15. A baya dai Miliyoyi kurum JAMB ta ke ba Gwamnati. An nemi Hukumar ta kashe Biliyan 2 daga cikin kudin da ta samu inji Benjamin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel