Ba kanta: An kama shugabannin PDP 5 a jiha guda bisa zargin kisa

Ba kanta: An kama shugabannin PDP 5 a jiha guda bisa zargin kisa

Hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ta tabbatar da kama wasu shugabannin jam’iyyar PDP na kananan hukumomi 5 bisa zargin kisan wani Borishade Adeniyi, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Apapa.

Wadanda aka kama din sun hada da; Injiniya Kehinde Fasasi, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Eti-Osa; Rotimi Kujore, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Lagos Island, Alhaji Fatai Adele, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Mushin, Mista Ismail Abiola, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Amuwo Odofin da Dakta Amos Alabi, shugaban jam’iyyar a karamar hukumar Surelere.

An kama shugabannin jam’iyyar ne bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Mista Edgal Imohimi, kuma tuni aka mayar da su sashen binciken laifuka na musamman domin cigaba da bincike a kansu.

Ba kanta: An kama shugabannin PDP 5 a jiha guda bisa zargin kisa

Ofishin jam'iyyar PDP na kasa

Rikici ya barke ne a wurin wani taron jam’iyyar ta PDP a jihar Legas da daga bisani ya rikide zuwa rikici day a kai ga har an harbi shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Apapa a kafa kafin daga bisani ya rasa ransa a wani asibiti da aka garzaya da shi.

Bayan samun rahoton abinda ya faru ne, kwamishina Edgal ya umarci a gaggauta kama dukkan shugabannin jam’iyyar ta PDP da suka halarci taron.

DUBA WANNAN: Farawa da iyawa: Wasu 'yan takarar PDP sun janye bisa zargin rashin adalci

Kazalika ya umarci shugabancin jam’iyyar PDP a jihar da ya gaggauta kwace makamai daga hannun shugabanninta ko su fuskanci fushin hukuma.

Ko a satin day a gabata saida hukumar ‘yan sanda ta kama wani dan majalisar dokokin jihar Legas, Dipo Olorunrinu, bayan samun sa da tare da ‘yan dabar sad a wasu manyan bindigogi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel