Batun kin shiga zaben PDP 2019: Dama kun san makomarku – APC

Batun kin shiga zaben PDP 2019: Dama kun san makomarku – APC

- Jam'iyyar APC ta kasa jure barazanar kauracewa zabe da PDP ta yi har sai da ta mayar da martani

- Sai dai martanin yafi kama da magar nan da ake cewa, ko a jiki na wai am mintsini kakkausa

Jam’iyyar APC ta mayarwa da PDP martani kan barazanar da tayi na kin shiga zaben 2019, inda ta ce dama barzanar kin shiga zaben ya samo asali ne don sun kwana da sanin cewa karshensu ya kusa.

Batun kin shiga zaben PDP 2019: Dama kun san makomarku – APC

Batun kin shiga zaben PDP 2019: Dama kun san makomarku – APC

Shugaban jam’iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomhole ne ya furta hakan a karshen makon da ya gabata yayinda yake karbar rahotan yadda zaben fidda gwanin da aka gudanar na gwamnan jihar Osun, daga hannun gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari.

Oshiomhole ya ce, “A duk lokacin da kaga zomo ya fito daga rami da maraice ba don mafarauci ya turnuka masa hayaki ba, ya ranta a guje cikin daji to tabbas kasan karshensa ne yazo, domin abinda ya koro shi daga ramin yafi wuta zafi”.

A cewarsa ‘yan Najeriya a baya sun gaji da salon tafiyar mulkin da PDP ta shafe shekaru 16 tana gudanarwa a lokacin farashin gangar mai guda na $140, sannan rashin tabuka abin azo a ganin da su kayi ne ya sanya APC ta hambarar da PDP daga kan kujerar mulkin kasar nan a wancan lokacin don haka yanzu ba su da wani abu sabo da za su iya yiwa ‘yan Najeriya.

KU KARANTA: PDP ta yi Allah-wadai da kona makarantar da sanata Dino Melaye ya gina

Ya cigaba da cewa jam'iyyar APC bata dauki zaben 2019 a matsayin a mutu ko ai rai ba, sai dai kawai jam’iyyar PDP ce ta kidime don ganin sun yanzu bata da makaman da take amfani da su wajen murde zabe kamar da, ta hanyar amfani da kudaden al’umma.

Wannan martani da Oshiomhole ya mayar na zuwa bayan da shugaban jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus yayi barazanar cewa jam'iyyarsu na iya kauracewa shiga zaben 2019 matukar za'a yi amfani da hukumar zabe mai zaman kanta da hukumomin tsaro don a murde zabubbukan shekara 2019.

Batun kin shiga zaben PDP 2019: Dama kun san makomarku – APC

Uche Secondus

Secondus ya fadi hakan ne bayan da jam'iyyar PDP ta bayyana zaben gwamnan jihar Ekiti da APC ta lashe a matsayin wani abu mai kama da fashi da tsakar rana.

A karshe shugaban jam’iyyar ya godewa gwamna Yari bisa amincewa da yin aikin sanya idanu kan yadda tsara zaben fidda gwanin a jihar Osun ya gudana kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar, sanann ya ce an kafa kwamitin karbar korafi ga duk wanda yake jin bai gamsu da yadda zaben ya kaya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel