Yadda muka shigo da Buhari siyasa ya ci amanar mu – Buba Galadima

Yadda muka shigo da Buhari siyasa ya ci amanar mu – Buba Galadima

Daya daga cikin fitattun 'yan siyasa a Najeriya kuma na hannun damar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a da watau Buba Galadima ya yi kaca-kaca da tsohon aminin nasa a wata fira da yayi da gidan jaridar Premium Times.

A cikin firar dai, Buba Galadima da ke zaman babban dan adawar shugaban kasar a yanzu kuma shugaban bangaren jam'iyyar APC da ta rabe gida biyu watau R-APC ya bayyana shugaban kasar a matsayin butulu da suka shigo da shi siyasa amma kuma ya ci amanar su.

Yadda muka shigo da Buhari siyasa ya ci amanar mu – Buba Galadima

Yadda muka shigo da Buhari siyasa ya ci amanar mu – Buba Galadima

KU KARANTA: Ku sadu da Abdulkarim Dauda Daura, babban mai tsaron lafiyar Buhari

Legit.ng ta samu cewa Buba Galadima din yace: Ni na fara kiran wani taro a garin Kaduna gidan surikin marigayi Abacha, Bashir Dalhatu, tare da wasu mutane 33 inda muka muka tattauna yadda Obasanjo ke cin zarafin iyalin Abacha a lokacin tare da batun shigo da Buhari cikin siyasa.

Haka zalika Buba Galadima ya kara da cewa, ya zuwa lokacin da aka rantsar da shi a 2015 ba ya tare da ko mutum daya daga cikin su 34 din nan. Duk ya zubar da mu, ya watsar da mu.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta ce tuni ta soma shire-shiren ta na maido da martabar Arewa musamman ma noma da kuma masana'antu irin masaku da kuma dalar gyada a garin Kano.

Kamar dai yadda babban Sakataren masana'antu da kasuwanci, Edet Akpan da Hajiya Aisha Abubakar ta wakilta ta ce, matakin farko da gwamnatin ta dauka shine na bude ofishin shiyya na kula tare da bincike kan harkokin noma na Nigeria Agribusiness and Agro-Industry Development Initiative (NAADI) a jihar ta Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel