Guguwar canji: Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu fiye 2000 a wata jihar kudu

Guguwar canji: Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu fiye 2000 a wata jihar kudu

A jiya, Asabar, ne shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus, ya karbi wasu jiga-jigan 'ya'yan APC da suka yi fatali da jam'iyyar.

Mutanen da suka hada da kwamishinonin jihar 8 da 'yan majalisar dokoki 3, sun bar jam'iyyar ta APC ne yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kaddamar da takarar sa a Yola.

A cewar Secondus, daga cikin kwamishinonin akwai zuwa Ibrahim Mijinyawa da Umar Daware.

Guguwar canji: Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu fiye 2000 a wata jihar kudu

Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu

A can kuma jihar Akwa Ibom dake kudu maso kudancin Najeriya, sabon shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya karbi wasu tsofin 'yan majalisar wakilai 2 da magoya bayansu fiye da 20,000 da suka fice daga jam'iyyar PDP.

Tsofin 'yan majalisar su ne; Bassey Etim da Esio Okwong. Sun kasance a majalisar ta wakilai ne daga shekarar 2003 zuwa 2007.

DUBA WANNAN: Damar karshe: Bukatu 7 da R-APC suka gabatarwa Buhari gabanin ganawar su ta karshe da APC a yau

Oshiomhole ya karbi tsofin 'yan majalisar ne a sakatariyar jam'iyyar APC dake Uyo, babban birnin jihar ta Akwa Ibom.

A jawabinsa ga sabbin 'yan APC din, Oshiomhole ya bukaci hada kai da tsofin 'yan jam'iyyar domin samun nasara a zabukan shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel