An yi zazzafar musayar wuta tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya, kowanne bari sunyi rashi

An yi zazzafar musayar wuta tsakanin Boko Haram da Sojojin Najeriya, kowanne bari sunyi rashi

- Kowa ya rasa nasa a wata gabzawa da akai tsakanin Sojoji da 'yan Boko Haram

- Mayakan Boko Haram dai sun matsaka kaimi wajen kaiwa Sojin hari a 'yan kwanakin nan

- Sai dai kuma duk yunkurin nasu baya kaiwa ga gaci, kasancewar ana bata kashi

Rundunar Sojojin Najeriya ta fitar da sanarwar cewa Sojojinta sun kashe 'yan Boko Haram da dama amma ita ma tayi rashin wasu daga cikin jami'anta a wata musayar wutar da suka yi da ‘yan ta’addan.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun yiwa sojin Najeriya kwanton bauna a Yobe

‘Yan ta’addan Boko Haram sun yiwa sojin Najeriya kwanton bauna a Yobe

Cikin zazzafar musayar wutar da ta biyo bayan wani kwantan bauna da ‘yan Boko Haram din suka yiwa sojojin a wani wuri da ake kira babban gida jiya Asabar, a garin da yake kusa da sansanin sojojin da aka taba kai wa hari a jihar Yobe.

KU KARANTA: Kaico: Wani lebura ya kashe Uban-gidansa tare da binne gawar don ya sace kudinsa

BBC ta rawaito cewa, akalla sojoji 28 ne suka rasa ransu a harin da aka kai a sansanin, inda kuma aka ruwaito mayakan na Boko Haram suka kwashi makamai. Amma rundunar sojin ta musanta kashe jami'anta a harin.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Texas Chukwu ya aike wa 'yan jaridu, sanarwar ta bayyana cewa mayakan sun yi wa sojin kwantar bauna ne bayan sun shigo babban gida domin neman abinci.

Duk da wasu daga cikin jami’anta sun rasa ransu, amma ta ci karfin mayakan na Boko Haram kuma yanzu kura ta lafa komai ya koma dai-dai.

Amma sai dai rundunar Sojojin ba ta bayyana adadin sojojin da aka kashe mata ba da kuma adadin mayakan Boko Haram din da suka mutu yayin artabun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel