Wasu tsirarun Mutane ke cin moriyar Gwamnatin Buhari - AYCF

Wasu tsirarun Mutane ke cin moriyar Gwamnatin Buhari - AYCF

- Kwanaki wasu Kungiyoyi su ka soki Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari

- Buhari ya maida martani yace barayi ne kurum ke kuka a Gwamnatin sa

- Wannan martani dai ya ba wasu Matasa a Arewacin Kasar haushi ainun

Mun samu labari cewa Kungiyar wasu Matasa da ke Arewacin Najeriya sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda su kace ya kamata a tika Buhari da kasa a 2019 domin ya gaza gyara Najeriya.

Wasu tsirarun Mutane ke cin moriyar Gwamnatin Buhari - AYCF

Shugaban Kungiyar Matasan Arewa ya caccaki Buhari

Matasan da ke karkashin lemar Kungiyar “The Arewa Youths Consultative Forum” sun ce Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta kowa ba ce face wasu tsirarun miyagu da ke cin karen su babu babbaka a Kasar.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku yayi wa APC illa a Arewa

A wani jawabi da Kungiyar tayi a Kaduna ta bakin Shugaban ta Yerima Shettima ta tabbatar da cewa Gwamnatin nan ba san abin da ta ke yi ba. A baya wasu Kungiyoyi a Kasar sun bayyana wannan a wani taro da aka yi.

Fadar Shugaban Kasa tayi wuf da maida raddi inda tace wasu Barayi ne da bata-gari su ke jin haushin yadda ake bin gaskiya da tsarin mulki a wannan Gwamnati. Sai dai Yerima Shettima yace wannan maganar banza ce.

Shugaban na Kungiyar Matasan Arewa AYCF ya soki kalaman Garba Shehu inda yace babu hankali da dattaku a cikin su. Shettima ya ayyana cewa ba shakka dole a tika Gwamnatin nan da kasa don ba Talaka ke morar ta ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel