Bukola Saraki na tunanin inda zai sa gaba bayan ya gana da Shugaban Kasa Buhari

Bukola Saraki na tunanin inda zai sa gaba bayan ya gana da Shugaban Kasa Buhari

A halin yanzu mun fahimci cewa Shugaban Majalisar Kasar nan Bukola Saraki ya shiga cikin wani mawuyacin hali inda wasu ke kira ya bar Jam’iyyar APC yayin da wasu ke neman ya tsaya. Wannan dai ne ya jefa Saraki cikin sarkakiya.

Bukola Saraki na tunanin inda zai sa gaba bayan ya gana da Shugaban Kasa Buhari

Shugaban Kasa Buhari na neman Bukola Saraki ya tsaya a APC
Source: Depositphotos

Wasu magoya bayan Shugaban Majalisar Kasar na kokarin ganin Saraki ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki. A wani bangaren kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya nemi Bukola Saraki yayi hakuri su zauna a Jam'iyyar APC.

Wasu manyan ‘Yan siyasa a kasar su na kira ga Bukola Saraki ya tattara ya rabu da APC a lokacin da manyan Jam’iyyar har da fadar Shugaban kasa su ke kokarin ganin Shugaban Majalisar Dattawan bai tattara ya koma Jam’iyyar PDP ba.

KU KARANTA: Dalilin kyakkyawar alaƙar shugaba Buhari da wani Gwamna a Kudu

Bukola Saraki ya gamu da rikici iri-iri bayan ya dare kujerar da ya ke kai. Fadar Shugaban kasa dai ba tayi wani kokari na ganin an dagawa Saraki kafa ba. Wasu na ganin don haka babu dalilin cigaba da zama a Jam’iyya guda da Shugaban kasar.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Magoya bayan Saraki a Majalisar Kasar da kuma Jihar Kwara su na ganin shigo-shigo babu zurfi ne Shugaba Buhari yake yi masa don haka su ka nemi yayi watsi da tayin Shugaban Kasar ya fice da APC tun da wuri.

Manyan ‘Yan Majalisa irin su Yakubu Dogara, da Sanatoci irin su Barnabas Gemade, Danjuma Goje, Suleiman Hunkuyi, Rabiu Musa Kwakwanso, da Adamu Ailero da su Gwamna Aminu Tambuwal na kokarin ganin Saraki ya fice daga Jam’iyyar .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel