Damar karshe: Bukatu 7 da R-APC suka gabatar gabanin ganawar su ta karshe da APC a yau

Damar karshe: Bukatu 7 da R-APC suka gabatar gabanin ganawar su ta karshe da APC a yau

Gabanin wata ganawa ta karshe da shugabannin tsagin R-APC zasu yi da shugabancin APC a daren yau, Lahadi, jaridar Tribune ta wallafa wani rahoto dake kunshe da sakon 'yan tsagin na R-APC.

Rahoton ya bayyana cewar shugabannin R-APC din sun mika wasu bukatu 7 da suke burin shugaba Buhari ya cika masu a matsayin dama ta karshe da zasu bawa APC da gwamnatin Buhari kafin su fice cikin sati mai zuwa.

Bangarorin biyu sun amince da yin wata ganawa da zata zama ta karshe a jerin ganawar yin sulhu da suke ta yi.

Ga jerin bukatun kamar yadda jaridar ta Tribune ta rawaito;

1. Tabbatar da dorewar Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattijai bayan zaben 2019.

2. Tabbatar da Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar wakilai bayan kammala zaben 2019.

Damar karshe: Bukatu 7 da R-APC suka gabatar gabanin ganawar su ta karshe da APC a yau

Buhari da Buba Galadima

3. Mayarwa da 'yan tsagin R-APC dukkan mukamansu da sabon zaben shugabannin APC ya tafi da su.

4. A rushe zaben shugabannin jam'iyyar APC a jihohin da aka samu rabuwar kayuwa yayin zabukan shugabannin jam'iyyar.

5. A sake yin zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa domin samar da shugabanci mai karfi.

DUBA WANNAN: Barazanar tsinkewar tsintsiya: Shugaba da Jagoran APC sun gana da tsofin gwamnonin arewa 3, hotuna

6. Mayarwa da duk 'yan tsagin R-APC tikitin takara ba tare da wani sharadi ko zaben fitar da gwani ba.

7. A janye dukkan wata kara da barazanar shiga kotu da 'yan tsagin R-APC.

Wata majiya ta bayyana cewar wani wakilci daga ofishin shugaban kasa ya gana da Sanata Danjuma Goje tare da yi masa alkawarin cewar za a sassauta shari'ar da ake yi a kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel