An kashe 'yan Najeriya fiye da na Iraki da Afghanistan a lokacin Shugaba Buhari - In ji Atiku

An kashe 'yan Najeriya fiye da na Iraki da Afghanistan a lokacin Shugaba Buhari - In ji Atiku

- Shirye-shirye sun kankama na fara yunkurin kayar da Buhari a 2019

- Har ma Atiku ya kaddamar da takararsa a birnin Yola

- A yayin kaddamarwar ya furata wasu kalamai masu kama da gugar zana ga gwamnatin APC

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman takarar shugabancin kasar nan a inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, yayi wani jawabi ga dimbin magoya bayansa a garin Yola na jihar Adamawa.

Inda a cikin jawabin nasa ya bayyana cewa babban abin da za’a tuna gwamnatin Muhammadu Buhari bayan shudewarta, shi ne kisa da zubar da jinin jama’a.

An kashe 'yan Najeriya fiye da na Iraki da Afghanistan a lokacin Shugaba Buhari - In ji Atiku

An kashe 'yan Najeriya fiye da na Iraki da Afghanistan a lokacin Shugaba Buhari - In ji Atiku

Atiku ya ce adadin mutanen da suka mutu a lokacin mulkin APC, ya fi wadanda suka rasa rayukansu a kasar Iraki da Afghanistan.

"An kashe mutane an zubar da jini, Najeriya tayi asarar rayuka masu yawan gaske a lokacin gwamnatin Jam'iyyar APC”.

Haka zalika tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ke fatan samun tikitin tsayawa takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya ce Buhari bai cancanci kasancewa jagoran al’umma ba, matukar dai ana batun kulawa da abubuwan da suka shafi cigaban ‘yan kasar nan.

KU KARANTA: Tsiyar nasara sai za shi gida: Zamu baku mamaki r-APC ga APC

Sannan ya kara da cewa wannan gwamnatin ita ce kan gaba wajen rashin samar da aiyukan yi tun da aka kafa kasar nan a tarihi, muna da matasa sama da miliyan goma da basu da aikin yi.

"Tunda aka kafa kasar nan ba'a taba samun rashin hadin kai a kasar nan ba kamar yanzu, saboda haka zan kawo karshen kashe-kashe da rashin aikin yi idan na samu damar hawa kujerar shugabancin kasar nan." A cewar Atiku Abubakar.

Taron wanda aka gudanar da shi a dandalin Ribado da ke Yola, ya samu halarcin shugaban jamiyyar PDP na kasa Prince Uche Secondous da sauran jigogin jam’iyyar.

A karshe ya bayyana cewa ya dawo cikin Jamiyyar ta PDP ne, domin nan ne gidansa na ainihi, tare kuma da cewa matukar jamiyyar PDP ta dawo kan mulki to babu shakka zata farfado da tattalin arzikin kasar nan tare da samar da tabbatacen tsaron da zai samar da kariya ga dukiya da rayukan al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel