Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

- Muna son mu san matsayarku, kuna can ne ko kuna nan?

- Jam'iyyar PDP ta bawa manyan jigogin siyasa wa'adin sati biyu don ta fara kimtsawa tunkarar zaben 2019

- Wannan shiri dai na da alaka da batun komen da yaki ci yaki cinyewa na 'yan R-APC

Jamiyyar PDP ta nuna wutar ciki akan batun dawowar yan sabuwar R-APC cikinta domin kammala dukkanin wata yarjejeniya.

Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

Fadan karshe: Jamiyyar PDP ta baiwa Saraki, Dogara, Tambuwal da Kwankwaso wa'adin mako biyu su yanke shawara

Tun da farko tsagin jamiyyar R-APC da PDP sun dauki makwanni suna tattaunawa domin samun mafita a zaben Shekarar 2019.

Amma sai ga shi shugaban kasa Muhammad Buhari tare da shugaban Jamiyyar APC sun kaddamar da wani shiri na neman sulhu tare da rarrashin fusatattun yan Jamiyyar da suka kira kansu da suna R-APC, da suyi hakuri su zauna a cikin jamiyyar ta APC.

KU KARANTA: R-APC zata iya tsayar da dan takarar shugaban kasa - Buba Galadima

Bisa wannan takaddamar ne jamiyyar PDP ta yanke hukuncin baiwa shugaban majalisar dattawa tare da na majalisar wakilai Yakubu Dogara, wa'adin mako biyu kan su dawo cikin jamiyyar ta PDP.

Sauran sun hadar da gwamanan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da na jihar Benuwe Samuel Orton, gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma sauran Mambobin majalisar dattawa da ta wakilai.

Sai dai wata majiya ta bayyana yadda aka gudanar da wani taro na musamman, jim kadan da ganawar da shugaban kasa ya yi da shugaban Majalisar dattawa ta kasa a ranar Alhamis. Inda su ka tattauna akan ficewarsu daga jamiyyar APC ko su zauna a cigaba da damawa da su.

Majiyarmu ta rawaito cewa, wannan sakon wa'adin makon biyun ya iske Bukola Saraki a ranar Larabar da ta gabata a garin Kwara a wata tattaunawar sirri tsakanin Sarakin da Nyesom Wike.

Yanayin siyasa na cigaba da daukar sabon salo musamman kan yadda ake samun yawaitar sauya sheka tsakanin jam'iyyun biyu gabanin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel