Buhari bai cika duka manyan alkawuran da ya dauka ba – Tanimu Turaki

Buhari bai cika duka manyan alkawuran da ya dauka ba – Tanimu Turaki

Wani tsohon Ministan Najeriya watau Kabiru Tanimu Turaki SAN ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yaudarar jama’ar kasar nan domin lashe zaben 2015 inda ya doke PDP. Turaki yace abubuwa ba su gyaru ba a Kasar.

Buhari bai cika duka manyan alkawuran da ya dauka ba – Tanimu Turaki

Dala da Kayan abinci da kudin fetur sun tashi a mulkin Buhari

Tsohon Ministan kasar Turaki yace sam Muhammadu Buhari ba shugaba bane ganin yadda ya saba alkawuran da ya dauka lokacin yakin neman zabe. Kabiru Tanimu-Turaki ya bayyana wannan ne a Garin Lafia da ke Nasarawa.

Sahara Reporters ta rahoto tsohon Ministan kwadago da kuma na ayyuka na musamman na kasar yana cewa Shugaba Buhari bai cika alkawuran da ya dauka na habaka tattalin kasa da kuma yakar Boko Haram da yaki da sata ba.

Kabiru Tanimu-Turaki ya bayyana hakan ne wajen wani taron PDP kwanan nan. Ministan na Gwamnatin Jonathan yace a mulkin su ne aka yi maganin Boko Haram har aka iya shirya zaben 2015 cikin zaman lafiya a kasar.

KU KARANTA: Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya shirya takara da Buhari

A cewar Tanimu-Turaki, sun yi tunani Shugaba Buhari ai gama da Boko Haram ne cikin watanni 3 rak. Turaki yace a fannin yaki da sata kuwa, ‘Yan PDP kurum aka tasa gaba inda ya kuma koka da cewa APC ta rusa tattalin Najeriya.

Daga cikin irin yaudarar da Buhari yayi, akwai maganar cewa ba zai je asibiti a Kasar waje ba inji Ministan na PDP. Bayan na Shugaba Buhari yayi alkawarin rage farashin abinci da na fetur sannan kuma a daidaita farashin Dalar Amurka.

Dala da Kayan abinci da kudin fetur duk sun tashi a mulkin Buhari. Kwanaki dai kun ji cewa wasu Manyan Malaman addini da ke Arewacin Najeriya sun nuna cewa za su marawa Kabiru Tanimu Turaki bayan zama Shugaban kasa a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel