Jam’iyyar PDP ta tsaida wanda zai kara da APC a zaben Jihar Osun

Jam’iyyar PDP ta tsaida wanda zai kara da APC a zaben Jihar Osun

Mun samu labari cewa Sanata Ademola Adeleke ya samu tutar takarar Gwamna a Jihar Osun a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP. Adeleke ya lashe zaben fitar da gwanin ne da kuri’a 7 kacal.

Jam’iyyar PDP ta tsaida wanda zai kara da APC a zaben Jihar Osun

Adeleke zai gwabza da ‘Dan uwan Tinubu a zaben Osun

Ba da dadewa ba mu ka ji cewa Jam’iyyar PDP ta tsaida wanda zai kara da Jam’iyyar APC a zaben Osun da za ayi kwanan nan. Ademola Adeleke wanda yanzu yake wakiltar Osun ta Yamma a Majalisar Dattawa ne PDP ta ba tuta.

A Afrilun bara Ademola Adeleke ya samu zuwa Majalisa bayan ‘Dan uwan sa da ke kan kujerar ya rasu. Sanatan dai yayi fice ne wajen tika rawa a wajen taron siyasa da na biki. Sanata Adeleke ya doke Akin Ogunbiyi a zaben da aka yi jiya.

Ademola Adeleke ya samu kuri’u 1, 569 ne a zaben inda shi kuma mai bi masa a baya watau Akin Ogunbiyi ya samu kuri’u 1, 562. Kuri’a 7 ce kurum ta raba gardama a zaben tsayawa takarar da aka yi a wani otel a babban Birni Osogbo.

KU KARANTA: R-APC zata iya tsayar da dan takarar shugaban kasa - Buba Galadima

Sauran wadanda aka shirya yin takarar da su sun hada da Adeola Durotoye, Adejare Rafiu Bello, Ayoade Adewepo, Jide Ezekiel Adeniji, Sanata Ogunwale Felix Kola, Akogune Lere Oyewumi, da Sanata Olasunkami Akanbi Abdulrasheed.

Gwamnan Bayelsa Seriake Dickson ne ya gudanar da zaben. Wasu dai sun ce an nuna fifiko a zaben. Yanzu dai Ademola Adeleke zai kara ne da Gboyega Oyetola wanda ake cewa ‘Dan uwa tsohon Gwamnan Legas watau Bola Tinubu ne.

Jiya ne mu ka samu labari cewa kujerar Gwamna Abdullahi Ganduje ta girgiza bayan da ‘Yan kasuwar Jihar Kano su ka nuna cewa za su ba wanda ke shirin tsayawa takara a PDP goyon baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel