Gwamnatin Buhari ta garkame wani ‘Dan jarida babu shari’a tun 2016

Gwamnatin Buhari ta garkame wani ‘Dan jarida babu shari’a tun 2016

- An rufe wani ‘Dan jarida tun shekarar 2016 a Gwamnatin Buhari

- Jami’an DSS na zargin cewa ‘Dan jaridar dai boyayyan Tsagera ne

- Yanzu an hana sa ganawa da Lauyoyin sa da Iyalin sa da Likitoci

A halin yanzu hekaru fiye da 2 kenan da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kama wani ‘Dan jarida mai suna Jones Abiri mai shekaru 50 a Duniya ba tare da an shiga kotu da shi domin ayi shari’a ba.

Gwamnatin Buhari ta garkame wani ‘Dan jarida babu shari’a tun 2016

Ana zargin Buhari da wuce gona da iri na daure wani 'Dan jarida

Wannan mataki da Gwamnatin Buhari ta dauka ya gamu da suka da kiraye-kiraye iri-iri daga Kungiyoyin Kasar da na Duniya gaba daya. Shekaru 2 da su ka wuce babu wanda ya ji labarin inda aka kai wannan Bawan Allah.

KU KARANTA: Hatsarin mota ta rutsa da wani Ministan Buhari

Jones Abiri mai aure tare da ‘Ya ‘ya 5 ya shiga hannun Jami’an tsaro na fararen kaya watau DSS tun kwanaki fiye da 700 da su ka wuce. Daga lokacin kawo yanzu, babu wanda ya gan shi cikin Iyalin sa da ma Lauyoyin sa.

Jiya aka cika shekara 2 da Jami’an tsaro su ka kama wannan ‘Dan jarida a gaban ofishin sa a cikin Garin Yenagoa da ke Jihar Bayelsa. Abiri shi ne ke buga Jaridar nan ta Weekly Source. Tun daga ranar har yau dai ba a gan sa ba.

Kungiyar nan ta Amnesty International tayi tir da yadda aka rufe wannan ‘Dan jarida aka hana sa ganin Iyalan sa da Lauyoyin sa da kuma Likitocin da ke duba sa. DSS na zargin cewa ‘Dan jaridar Tsagera ne a Yankin Neja-Delta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel