Yadda Tsohon Sufeto Janar, Marigayi Ibrahim Coomassie ya bayar da umarnin damuka da garkame ni gidan kaso na Kirikiri - Shehu Sani

Yadda Tsohon Sufeto Janar, Marigayi Ibrahim Coomassie ya bayar da umarnin damuka da garkame ni gidan kaso na Kirikiri - Shehu Sani

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana yadda tsohon sufeto janar Marigayi Ibrahim Coomassie, ya bayar da umarnin dakumar sa tare da garkame shi a gidan kaso na Kirikiri dake jihar Legas a shekarar 1995.

Sai dai Sanatan ya bayyana cewa, daga bisani kuma sun kasance aminan juna bayanan sallamar sa daga zama a gidan kaso.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana, Sanata Shehu dan gani-kashe-nin akidar Dimokuradiyya kafin shiga faggen siyasa, ya bayyana a shafin sa na dandalin sada zumunta inda ya hikaito rayuwar Marigayi Coomassie da ajali ya katse masa hanzari a ranar Alhamis din da ta gabata.

Sanata Shehu yake cewa, sun kasance aminan juna tare da Coomassie bayan an sallame sa daga gidan kaso na Kirikiri da har ya sanya ya rike sa tamkar Uba a gare sa.

Ya ci gaba da cewa, makonni kadan da suka gabata kafin mai yankan kauna tayi masa halin ta, ya ziyarci marigayi Coomassie akan gadon sa na jinya dake mahaifarsa ta jihar Katsina.

KARANTA KUMA: Babban Birnin Najeriya ya samu sabon Kwamishinan 'Yan sanda

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne aka gudanar da jana'izar tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda a mahaifarsa ta jihar Katsina bayan ya rasu a wani asibitin Amadi Rimi dake jihar a sanadiyar wata 'yar gajeruwar rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Sanata Shehu ya jajanta kwarai da aniyya inda a yayin mika sakon ta'aziyyar sa ya ce, marigayi Coomassie dattijon arziki ne mai matukar kishin kasa tare da kwarewa kan aiki da yake rokon Mai duka ya kyautata makwancin sa da kuma sakayya da gidan Aljanna a gare shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel