'Yan sandan bogi sun kashe jigon PDP a jihar Imo

'Yan sandan bogi sun kashe jigon PDP a jihar Imo

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashi da makami ne sun harbe daya daga cikin shugabanin matasa na jam'iyyar PDP a jihar Imo mai suna Chidi Eburuaja.

Kafin rasuwarsa, Eburuaja shine shugaban matasa na Owerre Nkworji, mazabar shugaban kwamitin harkokin banki da kudi, Jones Onyereri.

Wani dan uwansa da ya tabbatar da rasuwarsa, Emeka Njoku, yace marigayin ya tuka motarsa zuwa wani shagon sayar da magunguna kuma ana wajen ne wasu 'yan bindiga suka far masa.

'Yan sandan bogi sun kashe jigon PDP a jihar Imo

'Yan sandan bogi sun kashe jigon PDP a jihar Imo

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun kai farmaki a jihar Jigawa, sun bindige wani mutum mai shekaru 58

Majiyar tace, "Mutane uku sanya da kayan 'yan sanda ne suka far masa misalin karfe 8.45 na dare.

"Sunyi kokarin kwace masa motarsa amma da ba suyi nasara ba sai suka harbe shi.

"Da farko an kaishi Joint Hospital dake Amaigbo, amma daga bisani aka mayar dashi asibitin koyarwa na jami'ar Enugu inda ya mutu a safiyar yau Asabar."

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku ruwaito muku yadda wasu 'yan bindiga 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka harbe babban limamin garin Bachi dake karamar hukumar Riyom na jihar Filato.

Marigayi Alhaji Abdullahi Abubakar ba boyeye bane a jihar musamman yadda ya yi suna wajen kira a zauna lafiya da kuma hallartan taron sulhu tsakanin Fulani da 'yan kabilar Birom da masu sassan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel