Kungiyoyin yarabawa sun kare shugaba Buhari daga zargin kasa iya mulki

Kungiyoyin yarabawa sun kare shugaba Buhari daga zargin kasa iya mulki

- Shugaba Buhari ya saye zukatan yarabawa

- A siyasa su waye ke da wuyar shawo kai?

- A yanzu an maida hankali kan yadda kabilar Ibo zasu yi da Buhari a badi

Kungiyoyin yarabawa sun kare shugaba Buhari daga zargin kasa iya mulki

Kungiyoyin yarabawa sun kare shugaba Buhari daga zargin kasa iya mulki

Watau duk inda aka zaga a duniya siyasar Najeriya tafi kowacce sarkakiya, musamman ganin yadda kasar ke da jama'a masu tarin yawa, kuma masu mabanbantan ra'ayoyi, na kabila, siyasa, addini da bangare.

Kasar nan tana da jerin kabilu akalla 250, da kuma yaruka akalla 300. Amma a siyasa dole a hado kansu don samun damar tafiyar da mulki.

Kungiyar Yoruba Ronu Leadership Forum, ta mayar wa da kungiyoyin Afenifere ta yarabawa zalla, da ma ta arewa samarinsu da dattijansu, sai kuma ta kabilun Ibo, wadanda suka yi hadakar yin Alla-wadai da bangaren tsarin mulki na Buhari.

DUBA WANNAN: Sanatoci 21 masu niyyar sauyin sheqa

A cewar kungiyar dai, so kai ne kawai da makauniyar kiyayya ake yi wa dattijon shugaban, dominn kuwa babu kamshin gaskiya a batun nasu.

Shugaban dai na neman tazarce duk da a mulkinsa an kasa karas da Boko Haram, an kuma kasa shawo kan kashe-kashen kabilanci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel