Dalilin Kyakkyawar alakar dake tsakanin Shugaba Buhari da Gwamna Umahi

Dalilin Kyakkyawar alakar dake tsakanin Shugaba Buhari da Gwamna Umahi

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Ebonyi ta bayyana cewa, har ila yau akwai kyakkyawar alaka tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, David Umahi.

Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa wannan alaka ko kadan ba ta da nasaba da siyasa.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, gwamnatin ta yi wannan jirwaye mai kama da wanka a yayin da ake babatun gwamnan zai sauya sheka daga jam'iyyar sa ta PDP zuwa APC.

Kwamishinan labarai na jihar, Emmanuel Onwe, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Abakaliki da cewar wasu al'ummar jihar sun fahimci dangartar gwamna Umahi da shugaba Buhari ta wata fuska ta daban.

Mista Onwe yake cewa, wasu mutane na mamakin kyakkyawar alakar dake tsakanin shugaba Buhari da Gwamnan duk da kasancewar sa dan jam'iyyar adawa ta PDP.

Dalilin Kyakkyawar alakar dake tsakanin Shugaba Buhari da Gwamna Umahi

Dalilin Kyakkyawar alakar dake tsakanin Shugaba Buhari da Gwamna Umahi

Ya ci gaba da cewa, sabanin hasashen mutane dangane da alakar, shugaba Buhari bai taba neman gwamnan akan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, sai dai kawai alakar su da kusanci ta zarce bambancin akida ta jam'iyyar siyasa.

A cewar Mista Onwe, alaka da kusancin shugabanni biyu tana da nasaba ne dangane da yabawa kokarin juna na shugaban kasa da kuma gwamnan wajen kawo ci gaba cikin jihar da kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Akwai 'Yan gudun Hijira 34, 000 na kasar Kamaru a jihar Cross River - SEMA

Ya kara da cewa, shugabannin biyun sun yi tarayya da juna ta fuskar akidun gudanar da jagorancin gwamnati tare da yabawa juna.

Bugu da kari gwamnan yana kuma yabawa shugaba Buhari dangane da fafutikar sa ta yakar cin hancin da rashawa da kuma bunkasar tattalin arziki ta hanyar kawo sabon shafi kan harkokin noma a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel