2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

A ranar Alhamis ne dandazon mambobin majalisar wakilai karkashin jagorancin dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji a jihar Kano, Abdulmuminu Jibrin Kofa, suka ziyarci shugaba Muhammadu Buhari domin jaddada goyon bayansu ga takarar shi a 2019.

'Yan majalisar su 100 sun ziyarci shugaba Buhari ne a karo na biyu bayan wata ziyara da suka kai masa a ranar Asabar ta wancan makon.

DUBA WANNAN: Jarumin Fim ya ci al-washin lashe zaben gwamnan jihar sa

A jawabinsa, jagoran 'yan majalisar magoya bayan Buhari, Abdulmuminu Kofa, ya bayyana cewar babu gudu, babu ja da baya a aniyarsu ta goyon bayan takarar shugaba Buhari.

'Yan majalisar sun fito ne daga sassan Najeriya daban-daban.

2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

Abdulmuminu Kofa ke jawabi yayin ziyarar ta su

2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

Dandazon mambobin majalisar wakilai da suka ziyarci Buhari

2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

Dandazon mambobin majalisar wakilai ke son daukan hoto dab Buhari

2019: Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari domin jaddada goyon bayansu

Dandazon mambobin majalisar wakilai sun ziyarci Buhari

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel