Shugaba Buhari ya yaudari talakawan Najeriya - Inji wani dan takarar shugabancin Najeriya

Shugaba Buhari ya yaudari talakawan Najeriya - Inji wani dan takarar shugabancin Najeriya

Tsohon ministan kwadago a lokacin mulkin Jonathan kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 karkashin tutar jam'iyyar PDP, Alhaji Tanimu Turaki ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mayaudari.

Turaki yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da magoya bayan jam'iyyar ta sa ta PDP na jihar Nasarawa a garin Lafiya, babban birnin jihar a cigaba da rangadin da yake yi domin sada zumunci.

Shugaba Buhari ya yaudari talakawan Najeriya - Inji wani dan takarar shugabancin Najeriya

Shugaba Buhari ya yaudari talakawan Najeriya - Inji wani dan takarar shugabancin Najeriya

KU KARANTA: Buhari yayi alkawarin farfado da dalar gyada a Kano

Legit.ng ta samu cewa Turaki ya kara da cewa da shugaba Buhari yana yakin neman zabe, alkawura uku ya yi amma har yanzu ko daya bai samu ya cika ba sai dai kullum kiran da yake yi na cewa ba kudi wanda kuma ba gaskiya bane.

Yace alkawuran da Buhari yayi na samar da tsaro da farfado da tattalin arziki da samarwa da mutane aikin yi duk har yanzu ba ko daya da ya tabbata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel