Da dumin sa: An fatattaki 'yan Najeriya daga dakunan otel-otel din kasar Sin (Bidiyo)

Da dumin sa: An fatattaki 'yan Najeriya daga dakunan otel-otel din kasar Sin (Bidiyo)

Wani faifan bidiyo mai tayar da hankali dake yawo yanzu haka a kafafen sadarwar zamani a Najeriya na nuni ne da yadda wasu 'yan Najeriya suka yi cirko-cirko a saman titi a gaban wani Otel din kasar Sin biyobayaan umurnin jami'an 'yan sandan kasar.

Kamar yadda muka samu, an ce 'yan sandan kasar ta Sin ne suka bayar da umurni ga dukkan masu otel din kasar su fitar da 'yan Najeriyan dake cikin su saboda wani boyayyen dalilin da har yanzu ba'a bayyana ba.

Da dumin sa: An fatattaki 'yan Najeriya daga dakunan otel-otel din kasar Sin (Bidiyo)

Da dumin sa: An fatattaki 'yan Najeriya daga dakunan otel-otel din kasar Sin (Bidiyo)

KU KARANTA: Buhari bai kauna ta kwata-kwata - Wani Gwamna a Arewa

Legit.ng ta samu cewa wasu 'yan Najeriya din dai sun nuna matukar rashin jin dadin su game da wannan matakin da gwamnatin ta dauka kansu musamman ma ganin cewa su mutanen kirki ne da suka zo kasuwanci kawai.

A cikin faifan bidiyon haka zalika an ga wani jami'in gwamnatin Najeriya dake aiki a ofishin jakadancin kasar yana kwantar masu da hankali tare da shan alwashin bin kadin lamarin.

Ga faifan bidiyon dai, kamar yadda muka samu daga GossipsMill:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel