An kamo farfesan nan da ya nemi dalibarsa, kuma yanzu zai yi zaman kurkuku

An kamo farfesan nan da ya nemi dalibarsa, kuma yanzu zai yi zaman kurkuku

- Yayi mata waya ne yana ciinikin nawa zata bashi daga tsatsonta

- Ta tona shi ga duniya a whatsapp

- Ya kuka da kansa ya tsere, an kore shi daga aiki, yanzu kuma zaije sijin

An kamo farfesan nan da ya nemi dalibarsa, kuma yanzu zai yi zaman kurkuku

An kamo farfesan nan da ya nemi dalibarsa, kuma yanzu zai yi zaman kurkuku

Hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) a jiya tace shirye shiryen karar Mista Richard Akindele, farfesa a jami'ar Obafemi Awolowo, a zargin da ake mishi na yunkurin lalata da daliba wanda yayi sanadin korarshi aiki a jami'ar.

A bayanin da yayi wa manema labarai a taron da Youth Alive Foundation, ICPC da UKAID suka shirya, mai aiki a matsayin Chiyaman din ICPC, Mista Musa Abubakar, yace korar da jami'ar tayi wa farfesa Akindele bai wadatar ba.

Abubakar, wanda kwamishinan dake kula da ilimi na ICPC, Mista Mohammed Ashiru baba ya wakilta yace yunkurin karar Akindele da ICPC taso yi tun farko ta samu dakatarwa ne daga jami'ar, domin tace ta riga da ta sallami malamin.

DUBA WANNAN: Dalilin kamo Alhaji Grema a Borno

Ya kara da cewa ICPC ta binciko laifuka da yawa na rashin da'a wanda ya hada da neman daliban jami'a da malamai ke yi kuma bazata yi kasa a guiwa ba gurin karar duk wanda aka kama da laifin.

Yace "Na tabbatar kunsan abinda Farfesa Akindele yayi. Zamu kai shi gaban kuliya. Duk da jami'ar tace ta koreshi, muna dai son kaishi gaban kotu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel