Gwamna Bello ya tonawa Dino Melaye asiri a kan kone ajuzuwan da ya gina

Gwamna Bello ya tonawa Dino Melaye asiri a kan kone ajuzuwan da ya gina

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce Sanatan jihar Kogi ta yamma, Dino Melaye, bashi da wani tasiri a siyasar jihar.

A ranar Laraba ne aka kone wasu ajuzuwa hudu da Sanata Melaye ya gina a wata makarantar sakandiren mata dake Sarkin Noma a Lokoja, babban birnin jihar.

Da yake ganawa da manema labarai, gwamna Bello ya bayyana cewar Melaye kan iya kitsa kone ajuzuwan domin jama'a su tausaya masa.

Gwamnan Bello ya tonawa Dino Melaye asiri a kan kone ajuzuwan da ya gina

Gwamnan Bello ya tonawa Dino Melaye asiri a kan kone ajuzuwan da ya gina

DUBA WANNAN: Hajjin Bana: Yau za a fara jigilar maniyyatan Najeriya, duba hotuna

Gwamna Bello ya bayyana cewar babu hannun shi ko na magoya bayansa a batun kone ajuzuwan.

"Na yi Alla-wadai da kone ajuzuwan. Saidai kada jama'a su manta cewar Sanata Melaye mutum ne mai son haddasa rudu domin ko a baya ya shirya kaiwa kansa hari domin yiwa wasu sharri, a saboda haka ba zan yi mamaki ba idan ya shirya a kone ajuzuwan da ya gina," a cewar gwamna Bello.

Babu yadda za a yi a matsayina na gwamna dake wakiltar dukkan mutanen jihar Kogi na yarda a kone ajuzuwan da dalibai zasu amfana koda kuwa waye ya gina su."

Dangantaka tsakanin gwamna Bello da Sanata Melaye ta dade da lalacewa duk da kasancewar su abokan juna a baya.

Sanata Melaye ne ya shugabanci kwamitin karbar mulki da gwamna Bello ya kafa kafin a rantsar da shi amma daga baya sabani ya shiga tsakaninsu a kan rabon mukamai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel