'Yan fashi sun kai farmaki a jihar Jigawa, sun bindige wani mutum mai shekaru 58

'Yan fashi sun kai farmaki a jihar Jigawa, sun bindige wani mutum mai shekaru 58

Hukumar Yan sanda reshen jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar wani mutum mai shekaru 58 da wasu 'yan fashi suka harbe a karamar hukumar Dutse a jihar.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri ya shaidawa kamfanin dillancin labarai NAN a Dutse cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Yuli misalin karfe 7.05 na yamma a gidan marigayin dake unguwar Godiya Miyetti.

Ya yi bayyanin cewa 'yan fashin sunyi ta bin sahun mutumin ne har gidansa kuma su kayi kokarin yi masa fashi.

Dan fashi ya yi kisan kai a Jigawa, amma ya shiga hannu

Dan fashi ya yi kisan kai a Jigawa, amma ya shiga hannu

KU KARANTA: Tirkashi: DPO da wasu 'yan sanda sun lallasa Alkali da lauyoyi a kotu, duba dalili

"Sun harbe mutumin ne lokacin da ya lura suna biye dashi kuma ya yi ihu don jama'a su kawo masa dauki, daga nan ne suka harbe shi a ciki suka gudu.

"Jami'an 'yan sanda sun iso inda abin ya faru bayan an sanar dasu kuma sun dauki mutumin zuwa asibiti kuma a yanzu yana samun sauki," inji shi.

A cewar Jinjiri, an fara gudanar da bincike domin gano wanda su kayi yunkurin fashin domin a gurfanar dasu gaban kuliya.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa anyi wata mummunan gobara a kasuwar Terminus dake garin Jos na jihar Filato.

An ruwaito cewa sama da shaguna 200 sun kone kurmus sakamakon gobarar da ta faru a daren jiya Juma'a. A halin yanzu dai ba'a yi kiyasin dukiyar da akayi asara sakamakon gobarar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel