2019: Atiku ya kaddamar da yakin neman Zabe a yau Asabar

2019: Atiku ya kaddamar da yakin neman Zabe a yau Asabar

A yayin da guguwar siyasa tuni da riga ta lullube duk wani lungu da sako na kasar nan ta Najeriya, mun samu rahoton cewa, a ranar yau ta Asabar ne tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zabe.

Bayan tsawon watanni na tuntube-tuntube tare da ganawa da masu ruwa da tsaki da mambobi na jam'iyyar PDP, a yau Asabar tsohon mataimakin shugaban kasar ya fara fafata yakin sa na neman zaben kujerar shugaban kasa sakamakon gabatowar babban zabe na 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasar zai bayyana gaban dumbin al'umma a birnin Yola na mahaifarsa ta jihar Adamawa da tsakar ranar yau ta Asabar domin rarrashin fusatar su dangane da mulkin kama karya na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, tsohon mataimakin shugaban kasar zai yi shawagi tare da kewaye cikin birnin na Yola domin neman goyon bayan al'ummar sa domin cikar burin manufar da ya sanya a gaba.

2019: Atiku ya kaddamar da yakin neman Zabe a yau Asabar

2019: Atiku ya kaddamar da yakin neman Zabe a yau Asabar

Atiku dai tsohon ma'aikacin hukumar kastam ne da ya fara neman kujerar shugabancin kasar nan tun a shekarar 1993, sai dai a wannan lokaci ya kasance daya daga cikin wadanda suka sadaukar da kudirin su ga marigayo Moshood Abiola domin lashe zaben jam'iyyar su da SDP (Social Democratic Party).

A ranar Juma'ar da ta gabata ne ofishin sa na sadarwa ya bayyana cewa, Atiku yayin kaddamar da yakin sa na neman zabe zai kuma gabatar da tsare-tsaren sa na jagorantar kasar nan da zarar ya samu nasara a babban zabe.

Kamar yadda kafofin watsa labarai suka bayyana akwai yiwuwar tsare-tsaren tsohon mataimakin shugaban kasar su hadar da; inganta tattalin arziki, ilimi, lafiya da noma, sauya fasalin kasa da kuma ci gaban mata da matasa.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ta kwadaitar da Saraki kan zama a cikin ta

A watan Nuwamba na shekarar 2017 da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP bisa dalilai saniyar ware da jam'iyyar ta maishe shi kamar yadda ya bayyana.

Bayan tuntube-tuntube da neman shawarwarin makusanta, 'yan uwa da kuma 'yan Najeriya daban-daban a nan gida da kuma kasashen ketare, Atiku ya yanke shawarar fara gudanar da yakin neman zabe gadan-gadan karkashin inuwar lema ta jam'iyyar PDP.

Kafin bayyana kudirin sa a fili jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Atiku ya shafe tsawon watanni na shawagi tare da yawon zagayen jihohi da dama na kasar nan, inda yake ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel