Saraki da wasu gwamnoni 3 na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Saraki da wasu gwamnoni 3 na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Ko shakka babu jam'iyyar APC a musamman cikin wannan mako ta ci gaba da kai ruwa rana domin ganin ta dakile tare da hana yunkurin wasu jiga-jigan mambobin daga ficewa aga jam'iyyar inda zasu sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Kamar yadda kafofin watsa labarai musamman jaridun The Nation, This Day da makamantan su suka ruwaito, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis din da ta gabata ya gana tare da shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki domin sulhuntawa tare da rarrashin sa.

Binciken jaridar Legit.ng ya bayyana cewa, Saraki da wasu gwamnoni 3 na jam'iyyar ta APC sun gudanar da wani taro da shugabannin jam'iyyar PDP cikin birnin Ilorin na jihar Kwara a ranar Larabar da ta gabata domin neman a yi ma su wurin zama tare da karba hannu biyu-biyu.

Saraki da wasu gwamnoni 3 na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Saraki da wasu gwamnoni 3 na shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, gwamnonin ukun sun hadar da; Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, da kuma Gwamna Abdulfatah Ahmad na jihar Kwara.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, shugabannin jam'iyyar PDP da suka hadar da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da kuma shugaban jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, sun ribaci ziyarar jihar Kwara ne da zummar ta'aziyyar rasuwar Mahaifiyar wani jigo na jam'iyyar APC, Alhaji Abubakar Baraje.

KARANTA KUMA: Mata 'Yan siyasa sun fi gaskiya da rikon amana - Obasanjo

Rahotanni sun bayyana cewa bayan gabatar da ta'aziyyar su, shugabannin sun shiga ganawa da fusatattun na jam'iyyar APC inda wasu ke cewa sun jefe tsuntsayi biyu da dutse guda da hakan ya tabbatar da manufar ziyarar su.

A yayin haka kuma, shugaban kasa Buhari tare da wasu gwamnoni da jiga-jigai na jam'iyyar APC sun shiga taron lalama da rarrashin Saraki domin hana shi sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP da hakan ka iya janyo zagon kasa ga nasarar jam'iyyar su a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel