Jam'iyyar APC ta kwadaitar da Saraki kan zama a cikin ta

Jam'iyyar APC ta kwadaitar da Saraki kan zama a cikin ta

Akwai alamu masu karfin gaske dake nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin jam'iyyar sa ta APC, sun shirya bayar da tukwici mai ban sha'awa da kwadaitarwa ga shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Jiga-jigan na jam'iyyar ta APC sun yanke wannan shawara ta kwadaitar da Saraki domin dakilewa tare da hana yunkurin sa na sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, wasu jiga-jigai musamman kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, za su jagoranci zaman sulhu da fahimtar juna tare da shugaban Majalisar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, tuni shugaba Buhari tare da wasu gwamnoni na jam'iyyar suka tattauna da Saraki a wani taron rarrashin Saraki da aka gudanar cikin fadar shugaban kasa a ranar Juma'ar da ta gabata.

Jam'iyyar APC ta kwadaitar da Saraki kan zama a cikin ta

Jam'iyyar APC ta kwadaitar da Saraki kan zama a cikin ta

Sai dai Saraki ba tare da boye-boye ba ya shaidawa shugaba Buhari matsayar sa ta sauya sheka da ya sanya Tinubu ke ganin wannan babban abin kunya ne a gare sa da kuma jam'iyyar baki daya na zabtarewar wata muhimmiyar katanga ta ginin jam'iyyar.

Bincike da bankade-bankaden rahotanni da manema labarai suka gudanar ya bayyana cewa, shugaba Buhari, mataimakin Farfesa Yemi Osinbajo tare da wasu gwamnonin jam'iyyar ta APC sun yi iyaka bakin kokarin su na shawo kan Saraki.

Wata majiyar rahoto kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito ta bayyana cewa, akwai yiwuwar hakar ganawar a wannan karo ta shugaba Buhari da Saraki ta cimma ruwa.

KARANTA KUMA: Osinbajo zai gabatar da jawabai a taron kasuwanci da za a gudanar gobe Asabar cikin Birnin Dubai

Cikin tukwicin da jam'iyyar ta APC za ta yiwa Saraki domin hana shi ficewa daga cikin ta kamar yadda majiyar ta bayyana sun hadar da:

- Maishe shi kujerar sa ta shugabancin Majalisar dattawa a 2019.

- Yawan tuntube da sanya shi cikin muhimman shawarori na gudanar da mulkin kasa.

- Fahimta tare da inganta dangantaka da alaka tsakanin Majalisar tarayya da fadar shugaban kasa.

- Sake nazari akan matsalolin da nPDP ta zayyana a watannin baya.

- Gudanar da sulhu da fusatattun shugabannin nPDP.

- Gujewa maimaita kurakuran baya da suka janyo wannan matsaloli a halin yanzu.

Majiyar ta kara da cewa, Saraki ya bukaci a gabatar da wannan alkawurra cikin rubutu domin ya kasance shaida duk sa'ilin da yaudara za ta gindayo a gaba.

Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin jagorori, gwamnoni da wasu mambobi na jam'iyyar na cike da takaicin rasa Saraki zuwa jam'iyyar PDP da hakan zai janyo wani babban kalubale da rashin daidaito cikin jam'iyyar a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel