Osinbajo zai gabatar da jawabai a taron kasuwanci da za a gudanar gobe Asabar cikin Birnin Dubai

Osinbajo zai gabatar da jawabai a taron kasuwanci da za a gudanar gobe Asabar cikin Birnin Dubai

A ranar gobe ta Asabar ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai gabatar da jawabai a taron cinikayya da kasuwanci da za a gudanar a daular Larabawa cikin Birnin Dubai.

Babban hadimin sa na musamman kan harkokin hulda a manema labarai da kuma al'umma, Mista Laolu Akande, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai ranar Juma'ar da ta gabata.

A cewar Akande, Mataimakin shugaban kasar zai gabatar da jawabai ga jiga-jigan kungiyoyin kasuwanci da cinikayya na duniya daga yankin daular larabawa da kuma Afirka.

Osinbajo zai gabatar da jawabai a taron kasuwanci da za a gudanar gobe Asabar a birnin Dubai

Osinbajo zai gabatar da jawabai a taron kasuwanci da za a gudanar gobe Asabar a birnin Dubai
Source: Depositphotos

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, manufar wannan taro ita ce binciken gami nazari kan hanyoyin gudanar da kasuwanci ga kamfanoni da kuma cibiyoyi kasuwanci daban-daban a daular ta Larabawa da kuma Najeriya.

KARANTA KUMA: 'Yan takarar Kujerar Gwamna 8 na jam'iyyar PDP za su gudanar da yarjejeniya a jihar Kaduna

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan taro zai kuma kara dankon zumunta tare da kulla alakar dangartaka ta kasuwanci tsakanin Najeriya da yankin na Larabawa da zai taimaka kwarai da aniyya wajen inganta tattalin arziki.

Osinbajo wanda ya bar Najeriya a ranar Juma'a, ana sa ran dawowar sa a ranar Lahadi mai gabatowa kamar yadda hadimin sa ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel