Yan sanda sun kama mutane 117 kan kishe-kashen Zamfara

Yan sanda sun kama mutane 117 kan kishe-kashen Zamfara

Yan sandan jihar Zamfara sun ce sun kama mutane 117 da ake zargi da hannu a kashe-kashen bayan nan da aka kai Gusau, karamar hukumar Shinkafi da sauran yankunan jihar.

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu a bayyana hakan a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuli.

A cewarshi, an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani mamaya da tawagar IGP na musamman suka kai a ranar Alhamis, wanda ya kwashe tsawon sa’o’i da yawa.

Yan sanda sun kama mutane 117 kan kishe-kashen Zamfara

Yan sanda sun kama mutane 117 kan kishe-kashen Zamfara

Ya kuma bayyana cewa rundunar sun kama wasu yan fashi 72 wanda suka kware wajen amfani da ababen hawa marasa rijista wajen garkuwa da mutane zuwa mafakarsu, yainda aka kama ababen hawa marasa rijista 73 daga wurin su.

KU KARANTA KUMA: Jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kakkabe yan ta’addan Boko Haram a Bulagalaye da Kwakwa (bidiyo)

Rundunar ta kuma gargadi dukkanin masu laifi da su tuba su mika makamansu ga yan sanda ko kuma su fuskanci hukunci idan aka kama su.

Ya kuma bukaci mambobin jama’a da su ba yan sanda bayanai masu muhimmanci kan ayyukan yan ta’adda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel