Zambar Haraji: Ronaldo ya biya Fan 12.1m ga Kasar Spain

Zambar Haraji: Ronaldo ya biya Fan 12.1m ga Kasar Spain

Mun samu rahton cewa fitaccen tsohon dan wasan kwallon kafa nan na kungiyar Real Madrid, watau Cristiano Ronaldo, ya biya fan miliyan 12.1 kimanin Naira biliyan 5.6 kenan a kudin kasar nan ta Najeriya.

Ronaldo ya biya wannan makudan kudi ne domin gujewa zama a gidan kaso na tsawon shekaru biyu sakamakon dakumar sa da laifin zambar haraji da ya aikata.

Ronaldo domin bude sabon shafi a kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italiya, ya sauke nauyin bashin duk wata tara dake kansa domin yanke duk wata alaka da tsohuwar kungiyar sa ta Real Madrid da kuma kasar Spain.

A makon da ya gabata ne Ronaldo ya kammala sauyin sheka daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus inda ta saye shi kan zunzurutun kudi har na fan miliyan 100.

Zambar Haraji: Ronaldo ya biya Fan 12.1m ga Kasar Spain

Zambar Haraji: Ronaldo ya biya Fan 12.1m ga Kasar Spain

Legit.ng ta fahimci cewa, baya ga Ronaldo akwai manyan 'yan kwallon kafa da suka shiga makamancin wannan tasku na badakar haraji da suka hadar da; Lionel Messi, Javier Mascherano, Luca Modric, Alexis Sanchez da kuma mai horas da 'yan wasa na kungiyar Manchester United, Jose Mourinho.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ronaldo da gayya ya aikata wannan laifi ne na kauracewa biyan haraji a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014.

KARANTA KUMA: 27 Agusta: Shugaba Buhari zai kaddamar da sabon Filin Jirgin Sama na jihar Bayelsa

Ana zargin wannan badakala ta haraji na daya daga cikin musababbin da ya sanya Ronaldo ya bar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan da ya bayyana fushin sa karara yayin da hukumomin kasar ta Spain suka gurfanar da shi gaban kuliya sakamakon rashin biyan haraji.

Bayan mako guda da sauyin shekar sa zuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Ronaldo ya sauke nauyin duk wani bashi dake kansa tatas na tarar rashin biyan haraji tare da yunkurin yanke alakar duk wasu harkokin kasuwancin sa a kasar.

Bugu da kari Ronaldo ya sanya katafaren gidan sa dake kasar Spain a kasuwa kamar yadda jaridar La Finca ta bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel