Zaben jihar Ekiti: An gurfanar da mutane 10 kan laifin rabawa masu zabe kudi

Zaben jihar Ekiti: An gurfanar da mutane 10 kan laifin rabawa masu zabe kudi

Hukumar yan sandan jihar Ekiti ta gurfanar da mutane goma a kotun majistaren jihar dake Ado-Ekiti kan laifin baiwa masu zabe kudi domin zaben jam’iyyarsu a ranan Asabar da ya gabata.

Lauyan yan sanda, Femi Falade, ya bayyana kotu cewa sun baiwa mutane kudi ne domin kada kuri’arsu ga dan takararsu.

Falade yace wannan ya sabawa kafa na 30 (a) da 103 (b) na kundin tsarin zaben 2010.

Wadanda aka gurfanar sune, Olowosile Eunice, Ajayi Modupe, Ayodele Omolara, Suliat Habib, Udoh Anthony, Oyebola Kemi, Roseline Tunde, Odunayo Toyin da Babalola Esther.

Falade ya kara da cewa wadannan mutane sun rabawa mutane kudi ana gobe zabe a kasuwar Ojaoba da ke Ado-Ekiti.

KU KARANTA: Anci tarar ango da ya sanya abaya don bibiyar ko matarsa na zagaye shi tana bin samari

Wadanda aka gurfanar sun musanta wannan laifi da ake tuhumarsu da shi yayinda lauyansu, Mr Chris Omokhafe, ya nemi kotu ta basu beli.

Alkalin majistaren, Mr Adesoji Adegboye, ya basu belin N50,000 da kuma wanda zai tsaya musu.

Zaben jihar Ekiti: An gurfanar da mutane 10 kan laifin rabawa masu zabe kudi

Zaben jihar Ekiti: An gurfanar da mutane 10 kan laifin rabawa masu zabe kudi

An gudanar da zaben jihar Ekiti ranan Asabar, 14 ga watan Yuli 2018 inda tsohon ministan ma’adinai, Kayodde Fayemi, ya lallasa mataimakin gwamna jihar, Olusola Kolapo da tazarar kuri’u kimanin 19,000.

Masu lura da zabe sun bayyana cewa wannan zabe ya gudana cikin zaman lafiya da lumana amma dai rabe-raben kudi nay a bata abun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel