Jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kakkabe yan ta’addan Boko Haram a Bulagalaye da Kwakwa (bidiyo)

Jirgin yakin sojin saman Najeriya ya kakkabe yan ta’addan Boko Haram a Bulagalaye da Kwakwa (bidiyo)

Rundunar sojin sama dake gudanar da aikin operation lafiya dole, a ranar 15 ga watan Yuli sunyi nasarar kakkabe yan ta’addan Boko Haram da dama a Bulagalaye da Kwakwa, duk a jihar Borno.

Dukkanin nasarar da aka samu a wuraren biyu ya kasance sakamakon kokarin bin sahun yan ta’addan da sojin Najeriya ke yi bayan sun dakile harinsu a kusa da Bama.

A lokacin da suka samu rahoton harin sai sashin kwararru da jirgin yaki suka bazama don gano yan ta’addan dake tserewa.

A take, yan ta’addan da suka jeru a yankin Bulagalaye suka fara rarrabewa a ayinda suka ga yanayin harin. Don haka jirgin sojin ya fara saukar da bama-bamai akan yan ta’addan dake neman tserewa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

An kakkabe yan ta’addan yayinda aka lalata ababen hawansu da makamansu, wanda yayi sanadiyan tashin bakin hayaki.

Hakan ce ta kuma kasance a yankin Kwakwa.

Ga bidiyon a kasa:

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel