Obasanjo na son sake shugabantar Najeriya ne ta kofar baya – Oshiomhole

Obasanjo na son sake shugabantar Najeriya ne ta kofar baya – Oshiomhole

Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da neman kujerar shugaban kasa ta kofar baya.

Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuli, Oshiomhole ya bayyana Obasanjo a matsayin sakataren shiri mai daukar gajiyayyun yan siyasa domin sake dawowa mulki.

Obasanjo na son sake shugabantar Najeriya ne ta kofar baya – Oshiomhole

Obasanjo na son sake shugabantar Najeriya ne ta kofar baya – Oshiomhole

Ya yi watsi da rahotannin cewa jam’iyya mai mulki na fama da yawan masu sauya sheka, cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke fuskantar awan masu sauya sheka.

KU KARANTA KUMA: INEC ta saki tsarin lokacin zabuka 4 da zata gudanar

A baya Legit.ng a ruwaito cewa a ranar Juma’a, 20 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yanke shawarar sanar da kudirinsa na sake takara da wuri a watan Afrilu domin ya kwantar da hankula.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda a karbi bakuncin mambobin kungiyar magoya bayansa a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Ya gode mambobin kungiyar kan yadda suke tare da shi tsawon shekaru da dama ba tare da sun samu komai ba.

Buhari ya bayyana cewa kasancewar ya nemi takara sau hudu kafin yayi nasara, yana sane da abubuwan dake faruwa a mazabu daban-daban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel