27 Agusta: Shugaba Buhari zai kaddamar da sabon Filin Jirgin Sama na jihar Bayelsa

27 Agusta: Shugaba Buhari zai kaddamar da sabon Filin Jirgin Sama na jihar Bayelsa

Cikin zaman jiran tsammani, sabon filin jirgin sama dake yankin Amassoma a karamar hukumar Ijaw ta kudu cikin jihar Bayelsa da ake faman kirdadon sa, zai kammalu a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 2018 kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

Kwamishinan labarai da rahotanni na jihar, Mista Daniel Iworiso-Markson da kuma shugaba mai kula da jiragen sama na jihar, Kaftin Henry Ungbuke, sun bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a farfajiyar jirgin saman da ake ta faman gudanar da aikace-aikace.

Jagororin biyu sun bayyana cewa, wannan gawurtaccen aiki da gwamnatin jihar ta fara gudanarwa tun a shekarar 2012 da ta gabata karkashin jagorancin Gwamna Seriake Dickson,inda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar a ranar 27 ga watan Agusta.

Gwamnan jihar Bayelsa; Seriake Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa; Seriake Dickson
Source: Depositphotos

Mista Daniel ya ci gaba da cewa, wannan mashahurin aiki na biliyoyin Naira da filin jirgin saman ya lakume zai kafa tarihi tare da tabbatar da inganta tattalin arziki na jihar da kuma wadata ga al'ummar jihar.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Fashi ya sace Motoci 32 cikin shekaru 2 a jihar Ondo

Ya kara da cewa, akwai muhimmin tasiri na filin jirgin saman sakamakon ayyuka da dama da zai samar ga al'ummar jihar tare da hanyar samar da kudaden shiga masu tarin yawa da zarar aikace-aikace sun fara gudana gadan-gadan a cikin sa.

Kwamishinan ya yabawa kwazon gwamnan sakamakon jajircewarda hangen nesan sa wajen ganin wannan aiki ya tabbata duk da matsin tattalin arziki da kasar nan ta shiga a lokutan baya.

Kazalika Legit.ng ta fahimci cewa, wannan filin jirgin saman yana tantagwaryar yankin Neja Delta musamman yankin kabilar Ijaw da zai kasance abin alfahari a gare su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel